Saturday, November 14, 2009

ABUBUWAN DA KE KAWO SABANI A TSAKANIN MUSULMI

Tunda fari a matsiynmu na Musulimi kuma masu ikirari da bin hakikanin Abubuwan da Manzon Allah Muhammad { s.a.w.a} ya zo mana da su daga Allahu {swa} wato Al'kur'ni mai tsaki, na hukunce-hukunce, kuma ya fassara mana su ta hanyar Ayyukansa a aikace, Umurninsa a umurce, da kuma Abubuwan da yaga ana yi Muraran kuma bai hana ba.da kuma dungurungun din Ayyukansa masu Al'barka wato {Hadisai} sahihai.

To, tunda kuwa har hakanne to bai kamata kullum mu dosa tsuke tunaninmu, muna kuma takaita kawunanmu ba. Idan mukayi haka to sai dan kankanin abu ya bamu wahalar ganewa {Wankin hula sai ya kaimu dare}

Da farko dai tunda Allah {swa} ya ce ''kasanni kafin ka bauta mani'' to gaskiya akwai wani abu da yakeyawan faruwa wanda kuma idan aka yi sake ana kallonsa to, a irin tawa fahimtar ba karamar Illa zayyi ba.musamman ga Ire-ire na marasa Ilimi wanda shi wannan abu bawai ya kai ya kawo bane.amma kuma an kasa fahimtarsa,sakamakon takure kwakwalwa da kuma tsuke tunini, gami da takaita bincike da kuma kebe iya Malaman da za'a yi karatu, fatawa ko tambayoyi a wurinsu ko kuma huldar arziki da su.rashin samun irin wadannan fahimtar juna da kuma tsuke tunanunnuka duk shi ya haifar da rashin fahimtar hakikanin wannan kalmar, da ma'anarsa a luggace da kuma hakikanin abin da Addinin Musulunci ke nufi a duk lokacin da aka ambaci wannan kalmar. da kuma irin abinda manzon Allah ke magana akai har wannan kalmar ta shigo.menene a farkon maganarsa?, kuma ya aka yi wannan kalmar ta shigo?, kuma mene ya fada a karshen maganarsa da har aka sami wancan kalmar aciki? ta yadda za'a auna da hankali kuma ya taimaka wajan fahimtar gaskiya don rarrabe shi daga gurbatatccen fassarar da ake wa wannan kalmar. domin shi shari'ar Musulunci dai-dai da hankali yake, ba sabanin hankali ba..domin idan har ya zama sabanin hankali to, ya zama dai-dai da hauka kenan kuma hakan bashi yuwuwa.mai karatu a auna wannan wannan magana tawa a ma'aunin hankali a gani, Idan magana ta saba da hankali to don Allah a gaggauta yi mani raddi, Idan kuma magana ta dace da hankali to don Allah a fada wa Duniya kowa ya ji.a jarida ne, a'a Rediyo ne, TV ne, ko a 'Internet'. domin masu daukan wannan kalmar mai saukin fahimta suna yi mata akasin fassara ko ince {kudin goro} wajen fassarar, to a gaskiya shawarar da zan basu shine su zurfafa nazari, kuma su fadada tunani a Addinance domin gaskiya da ni banyi niyyar cewa komai akan fassarar kudin goro da kuma fahimta ta akasi da ake wa ita wannan kalmar ba. to, amma da na tuna da wani hadisi na Manzonn Allah da yake cewa '' Idan kaga abin ki to ka kawar da Hnnuwanka, Idan har bazaka iya ba, to ka hana da Baki, Idan shima ya gagara to sai ka ki abin a zuciya. amma shine mafi raunin imani'' sa'annan kuma na tuna da cewa ''Musulmi dan uwan musulmi ne'' sai naga ya hau kaina bisa tilas in fadi abinda na fahimta wanda kuma nake ganin shine dai-dai, don in sauke nauyin da ya hau kaina.

Jaridar gaskiya ta fi kwabo na Ranar Alhamis 18 ga watan Yuni, zuwa Lahadi 21 ga Watan Yunin Shekarar 2009.a shfi na biyar, an buga wani Huduba na daya da na biyu a shafin HUDUBA mai taken '' Allah ya halasta Aure ga bayinsa''da wani limami ya gabatar. a gaskiya Malamin ya kware wajan tsara shimfidan Huduba, da kuma tsara Huduban mai ma'ana.musamman a janibin Aure da kuma sharuddan yinsa wannan kam tubarkalla!.

Sai dai kuma kash! na dade ina mamakin wata magana da Malam ya kawo a cikin shimfidar Hudubarsa duk da cewa Hdisine, to amma Malam ya dan tsuke fahimtar da Allah ya ba shi wajan fahimtar hakikanin ma'anar wannan Hadisin. Inda Malam ke cewa {Duk fararren abu bidi'a ne kuma duk bidi'a batace, kuma ko wacce bata makomarta wuta} to ina so in dauki wannan Hadisi in dan yi magana akai domin mu sami saukin fahimtar Hakikanin wannan Hadisin. to a gaskiya ni ba haka na fahimci ma'anar wannan Hadisin ba. kuma kamar ka fadi yadda ka fahimci kalmar '' kowacce bidi'a batace'' to shine nima naga ya kamata nima in fadi yadda na fahimci cewa lallai ba kowacce bidi'a bace bata.a addinance da kuma a zamanance, amma da Hadisan Manzon Allah Mohammad {saw} don kada ayi ta jefa musulmi cilkin rudani.lallai Manzon Allah {SAW} a cikin ar'ba'una hadis a hadisi na 28 wanda tirmizi da abu dauda suka ruwaito, Abi Nijahin Irbadhi ibn sariyata {RA} ya ce, ''Manzon Allah {SAW} ya yi mana wa'azi zukatanmu sun girgiza, Idanuwanmu sun kadu sai muka ce ya Manzon Allah {SWA} wannan wa'azi kamar wa'azin bankwana? sai kayi mana wasiyya! sai Manzon Allah yace''inai muku wasicci da jin tsoron Allah madaukaki, mabuwayi da kuma ji da biyayya koda an nada muku amiri bawa {Shugaba} kumsani fa wanda yayi tsawon rayuwa acikinku da snnu fa zai ga sabani mai yaw. na horeku da biyayya ga sunna ta, da sunnar halifofina shiyayyu masu shiryarwa ku yi ruko da ita da hakorar kuryar baka {ruko gam-gam} kuma kashedinku da fararrun kirkirarrun al'amura,domin duk kirkira bidi'ace kuma dukkanin bidi'a batace kuma dukkanin bata tana cikin wuta''

To, 'yan uwana musulmi yanzu zan dauki wannan hadisin in yi mata sharhin hakikanin abinda Manzon Allah ya ke nufi a wannan hadidin {a nawa mahangar} amma bisa dogaro da wasu hadisai da kuma wasu ayoyin Al'kur'ani da kuma wadansu maganganu da zan kawo a tawa mahangar. lallai wannan magana da manzon Allah yayi kasantuwarsa baya fadin magana son ransa sai abinda Allah yayi nufin ya fadi, to mu mun tafi akan cewa Allah ya sanar da shi abinda zai faru na sabawa ummurninsa a halifanci bayansa domin shi yasa ya ce '' wanda yayi tsawon rai a cikinku to da sannu zai ga sabani mai yawa'' to, Malam idan zaka yi wa kanka adalci kasan sabanunnuka sun faffaru da kuma rikicewar al'amura bayan rasuwar Manzon Allah {SAW} kamar yadda na ce shi Ssshehu Tijjani jikane ga manzon Allah {SAW} To, ga yadda nasabhar take;- dan Muhammad, dan Mukhtari, dan Ahmadu, dan Muhammadu, dan salimi, dan Abil-idin, dan salimi na biyu, dan Ahmadu, dan Ahmadu na biyu,Aliyu, dan Abdullahi, dan Abbas, dan Abdul-jabbari., dan Idrisu, dan idrisu na biyu,dan Ishaka, dan Zainul-abidina,dan Ahmadu, dan Muhammadu, dan wanda ake yi wa klakabi da { Nafsuzzakiyya}, dan Abdullahi-kameel, dan Hassanul-musanna. dan Husaini, dan Ali Ibn

Ga kadan daga kissar yadda Manzon Allah ya nadawa wannan Al'ummar Shuwagabanni har zuwa karshen duniya.ko Malam na so ya ce Annabi bai san cewa za'a yi watsi da maganarsa bane? har da ya ce'' ko da an nada muku amiri {Shugaba} bawa? har idan bai san cewa za'a sabawa ummurninsa ba to yaya za'ayi ya ce '' wanda yayi tsawon rai a cikinku da sannu zai ga sabani mai yawa? ko kuwa ba'ayi sabanunnuka akan halifanci bayan Manzon Allah bane? an ba wanda Manzon Allah ya ce '' Shine shugaba bayansa shugabancin? ko an hana shi?

MANZON ALLAH {SAW} YA NADA HALIFANSA KAFIN YA BAR DUNIYA!!!
Manzon Allah ya sa aka yi shela cewa '' Duk wanda yayi imani kuma ya yarda da ranar karshe, to idan ya sami iko to ya zo aikin hajji. da aka zo aka kare aikin hajji bayan kowa ya fara komawa hanyar garinsu, sai Manzon Allah ya aika da masu shela cewa ''Duk wanda ya tafi ya dawo, kuma masu fitowa daga Makka sai ya zama duk an taru a kusa da wata tafki da ake cewa 'Gadir kum' wato tafkin gadir an ce kimanin mutane dubu saba'in ne 70,000 suka taru a wannan wuri, amma wasu malaman tarihi irin su Tha'labi a tabsirinsa, da kuma sibt Ibn Jauzi a littafinsa Tadhkiratul-ukhasasil-ummah-fi ma'arifati A'immah da wasu sauran Malaman sunce matane dubu dari da ashirin ne suka taru.da Manzon Allah ya iso sai ya sa aka jera masa surdunan rakumai da dawakai ya hau. bayan yayi maganganu kan abubuwa da dama, sai ya ce wa mutane ''Ashe ba nine na fi can canta a bisa kawunanku ba?sai suka amswa eh! hakane!. Ahzab { 33;6}
Sai Manzo ya ummurci Ali {AS} da ya hawo wannan munbarin da yake kai da ya hau sai Manzon Allah ya kama hannun Ali {AS} ya daga ance har ana iya ganin farin ko hasken hammatan Manzon Allah {saw} sannan ya ce '' Duk wanda ya yarda ni Annabibsa ne, to bayana Ali ne shugabansa. sannan kuma bai gushe ba sai da ya lissafo shuwagabannin Al'ummah goma sha biyu wato tun daga Ali har zuwa Imamu Mahdi {AF} sannan kuma yayi addu'a mai tsawo inda yake cewa ''Allah ka tai maki wanda ya taimaki Ali,kuma ka cutar da wanda ya cutar da shi. daga nan sai aka sakko, ya ce ''kowa ya yi wa Ali Mubaya'a, wanda ya fara yi wa Ali mubaya'a shine Ummar {RA} sai Abubakar {RA} sai Usmanu {RA} sai Thalha da Zubairu sai sauran jama'a suka biyo ana ta mubaya'a Manzon Allah na cewa''Duk wanda ya warware ya warware don kansa''
sai kawai ga wannan ayar ta saukko ''lalle wadanda ke yi maka mubaya'a, Allah ne kawai suke yi wa mubaya'a, hannayen Allah na bisa hannayaensu, saboda haka wanda ya warware to yana warwarewane akan kansa kawai,kuma wanda ya cika ga alkawarin da yayi wa Allah a kansa, to, {Allah} zai kawo masa ijara mai girma'' suratul Fat'h aya ta-10


kuma kada mu manta lokacin da Manzo ya na nasabta Ali a Halifansa bayan shi sai da ya lissafa halifofin nan daya bayan daya har na karshen imam mahdi.Manzon Allah ya ce '' Bayan shi sai Ali, bayan Ali sai Hassan, bayan Hassan sai Husaini, bayan Husaini sai Ali dan Husaini, sai Muhammad dan Ali,sai Ja'afar dan Muhammad, sai Musa dan Ja'afar, sai Ali dan Musa, sai Muhammad dan Ali, sai Ali dan Muhammad,sai Husaini dan Ali, sai na karshensu Muhammad {Mahdi AF}

Ga littafai shabiyu 12 da suka tabbatar da hadisin nasabta Ali {AS} a matsayin khalifan Manzon Allah da Manzon yayi a tafkin Gadirv na daya Imam Fakhu'd -din-razi tabsirul kabir Mafatihul-gaibi, na biyu Imam Ahmad Thalabani tabsirul-kshaful-bayan, na uku jalluddin suwidi tabsirisa na Durrul manthur. sai na hudu, Abul-hasan Ali ibn Ahmad wahidi Nishapuri Asbabul-nuzul. sai na biyar Muhammad ibn jarir Thabarani tabsirinsa na tabsirul-kabeer sai na shida,Hafiz abu ni'aim isphani-ma nazal minal-Qur'an fi ta'arikh, bugu na 1 shfi na 375. sai na takwas shawahidatul-tanzil sai na tara ibn munanzil. na goma Bukhari. sai na shadaya musnad Ahmad. sai na shabiyu Ibn hibbana. duk wadannan littatafai daga wandanda suka kawo batun gadir sai wadannda suka kawo batun can-cantar imam Ali {AS} a matsayin halifan da manzon Allah na farko da ya nada kafin ya bar Duniya.

Sai maganar shuwagabanni 12 bayan wafatin manzon Allah {SAW} ga wadasu daga cikin littafan, kuma daga littafan sunni.sahih muslim juzu'i na 6 shafi na 3-4 babin Annasu Taba'u lil-kuraishh cikin littafinsa na A l'imara. na biyu a duba a duba sahihul-buhari.babi na hudu shafi na 165 a littafin hukunce-hukunce. na uku sai tirmizi babin ma ja'a fil khulafa'i. sai babi na hudu,al'fitan juzu'i na 6 shafi na 66-67. sai na biyar abu dauda cikin sinan dinsa juzu'i na 4 shafi na 106.sai na shida littafin al'mahdi hadisi na 4279 sai na bakwi Ahmad ibn hambal cikin musnad dinsa juzu'i na biyar shfi na 86-90, da kuma shafi na 92 -101 da shafi na 106-108. aje a duba wannan littatafan duka kuma ruwawyoyin sunna ne.duk sun tabbatar da batun khalifancin khalififin nan 12 bayan manzon Allah kuma da umunin manzon Allah. { ga yadda yace za'a yi kuma aka ki yi}ko kuwa saba wa manzo ma sunna ce? amma dai munsan cewa abinda manzo yayi, da wanda ya cewa ayi da kuma wanda yaga ana yi kuma bai hana ba sune sunna, daga nan kuma sai wanda ya kirkiri kyakkyawar aiki mai kyau ne ko maras kyau kowa yana da sakamakonsa dai-dai da shi.

Idan muka koma cikin wancan hadisin lalle manzo yace ''ya horemu da bin sunnarsa da bin sunnar khalifofinsa masu shiryarwa.ya ce kuma muyi ruko da ita gam-gam''to, lalle wadannan khalifofin nasa masu shiryarwa yana nufin wadancan khalifofin nasa ne guda 12 da muka kawo sunayensu da kuma littafan da suka tabbatar da anyi hakan daga sunni. Tambaya anan itace to an riki wadannan khalilfofin su 12 kamar yadda manzon Allah ya umurcemu da muyi? ko aiki da magamnan mazo ba sunna bace?.

Idan bamu mantaba a wanna hadisin saida manzo ya fara da cewa '' Abi sunnarsa'' tambaya;- shin anbi sunnar tasa?
ko kuwa akwai wata sunnar da ta shige ta manzon Allah ne? manzo ya ce bayana sai wane, sai wane, sai wane. ya ce ayi kaza, ayi kaza, ayi kaza to an yin? Tambaya;- waye mai bin sunnar manzo sak wanda ya aikat maganar manzo ko wanda ya barta?

GA WASU AYOYIN AL'KUR'NI DA HADISAI MASU FARLANTA DA KUMA SUNNATA ABINDA MANZO ALLAH YA ZO MANA DA SU.

Lalle abin koyi mai kyau ya kasance gareku, daga manzon Allah,ga wanda ya kasance yana fatan rahamar Allah da ranar lahira. kuma ya ambaci Allah da yawa--suratl azhab aya ta 21.
wannan domin lalle su,sun sabawa Allah da manzonsa, al'hali kuwa wanda ya saba wa Allah to lalle Allah mai tsananin ukubane---suratl-hashari aya ta 3-4.
abinda Allah yasa ganima ga manzonsa daga mutanen kauyukan nan, to na Allah ne kuma na manzonsa ne,kuma na masu dangantaka, marayu, da dan-hanya {matafiyi} ne, domin kada ya kasance abin shawagi a tsakanin mawadata dagcikin ku,kuma abinda manzo ya baku to ku karbeshi, kuma abinda ya hane ku to ku barshi. kuma kubi Allah da takawa, lalle Allah mai tsananin ukubane---suratul-hashari-aya ta 6-7.

An karbo daga Abu huraira Abdurrahaman dan sabri {RA} ya ce naji Manzon Allah yana cewa ''abinda na horeko ku nasanceshi, kuma abinda na ummurceku ku yi shi gargwadon ikonku.hakika abinda ya halakar da mutanenda kegabaninku shine yawan tambayoyi da sassabawansu ga annabawansu Buhari da muslim ne suka ruwaito a hadisi na 9 cikin ar'ba'una hadis.

A wani hadisin kuma manzon Allah {SAW} yana cewa '' Ina ji an kusa akirani in amsa kira { wafati}. don haka lalle ni mai barine a cikin ku, nauyaya biyu littafin Allah {Al'kur'ani} da kuma tsatso na. shi littafin Allah wato igiyace mai karfi daga sama zuwa kasa. su kuma tsastona iyalan gidana {Ahlul-bait} kuma hakika mai bada labari ya bani labari. lalle su, su biyun nan bazasu taba rabwa ba hai sai sun riskeni a bakin Tabki {Al'janna} to,kuyi dubi { nazarin } yadda zaku tafiyyadda su a bayana'' a wani hadisin na daban kuma ba zaku taba bata ba matukar kuyi ruko da su su su biyun nan. an karbo wannan hadisin daga fiye da mutane 20 daga cikin sahabban manzon Allah {SAW}. kuma an ruwaito daga masu ruwaya a cikin sahihul-muslim bugu na 2 shafi na 238. da musnad Ahmad ibn hambal bugu na biyar shafi na 181-182 da kuma shafi na 199-210 bugu na 1 cikin littafin Nafahatul-azhar-fi-khulasatul-abaqatul-anwar.

Sannan kuma manzon Allah ya ce '' misalin iyalan gidana kamar misalin jirgin ruwan Annabi Nuhu {AS} ne Duk wanda ya hauta hakika ya tsira. duk wanda ya barta hakika ya halaka. an karbo wannan hadisin daga sahabban manzon Allah su 8, da mutane 8 daga Al'majiran sahabban,da kuma sanannun malamai 60. da kuma fiye da marubuta 90 daga makarantar Ahlussunnah. an kuma bayyana shi a littafin Mishkatul-misabih shfi na 523. da kuma Ahmad ibn hambal a littafinsa na fara'idussumtayin bugu na 2 shafi na 242, ya kuma zo a Assawaqi'ul-muharragah shfi na 234.sai kuma littafin Uyunul-akbarbugu na 1 shafi na 211; sai littafin Nafahatul-azhar bugu na 4, shafi na 127.Duk wadannan manya-manyan litattafai duk sun gaskata abubuwanda muka fada kuma mafiya yawan wadannan littfafn duk ruwayoyin sunni ne. wadanda suke nuna umurnin Allah kan bin manzon Allah {SAW} da kuama kalaman manzon Allah masu al'barka. inda yake ta nuna a bishi, shi da iyalan gidansa tsarkaka wato { Ali, Fatima, Hassan, da Husaini AS} tunda ummurnin manzo sunnace me yasa ba'a nada Imam Ali {AS} a matsayin khalifan manzo na farko ba, kamar yadda manzon yayi ummurni to anyi hakan?.mai yasa aka ki yarda da batun kahlifofin nan 12 bayan ansan kuma lalle manzo yayi umrurni da hakan?.
To, wanda duk ya kauda kai daga maganan manzo, kuma ya bijirewa umurninsa, sannan kuma ya ki iyalan gidan manzon Allah, bayan kuma manzo ya ce '' a so su abi sunnarsu'' don Allah wanda yayi wannan Shine Ahlussunnah?
To, amma kamar a wasu darikun sufaye irinsu Shaikh Ahmadu Tijjani { RA} da dukkan wani dan uwa miusulmi na gari mai kaunar manzon Allah da iyalan gidansa tsarkaka kuma yake bin kur'ani da kuma umurnin manzo sau da kafa ai shine { Babban ahlussunnah} na hakika. ire-iren su shehu Ahmadu Tijjani { RA} sanin kowane ba wai ya tsayane a son manzo da iyalan gidansa ba kadai, shi kansa ma shrifin ne kuma shima yayi bayanin khalifofin nan 12 a cikin littafinsa na Ahzab-wsal-aurad kuma sai da ya lissafo sunayaensu daya-bayan-daya yana tawwassuli da su. kenan shehu tijjani ya sansu kuma ya yarda manzo yayi umurni da abi su sau da kafa. don haka abayyane take shehu Tijjani ya ji maganar kakansa { Manzon Allah} kuma yayi aiki da ita.tunda idan ka aikata maganar manzon Allah kayi sunna to lalle shehu tijjani {RA} ahlussunnane ba ma a sahun baya-baya yake ba. idan kace don me ?sai mu ce maka don ya aikata umrnin manzon Allah ta hanyoyi da daman gaske {don ya yarda da umurnin manzo na bin khalifofin nan 12 } kuma babu sunnar da ta wuce aikata maganar manzon Allah {SAW} to lalle shehu Tijjani a ahlussunne ba ma a sahun baya-baya yake ba. idan kace don me? to, sai mu ce maka don ya aikata umurnin manzon Allah ta hanyoyi da daman gaske { don yayi aiki da maganar manzon Allah} kuma babu sunnar da ta wuce aikata maganan manzo Allah.kamar yadda nace shi shehu Tijjani shi jikanne ga manzon Allah MUHAMMAD {SAW} Shi shehu tijjani dane ga Muhammadu, dan Mukhtari, dan Ahmadu, dan Muhammadu, dan Salimi na biuy, dan Abdil-Idin,dan salimi na biuy, dan Ahamad, dan dan Anmadu na biuy, dan Aliyu, dan Abdullahi, dan Abbas, dan Abdul-jabbari, dan Idrisu,dan Idrisu na biuy, dan Ishaka, dan Zainul-Abidina, dan Ahmadu, dan Muhammadu, dan wanda ake yi wa lakabi da {Nafsuzzakiyya} dan Abdullahil kamil, dan H assanul-musanna, dan Husaini, dan Ali ibn Abi Thalib na wajen nana Fatima 'yar Manzon Allah Muhammad {SAW} sabods haka da masu goyon bayan iyalan gidan manzo da 'yan Darika lalle duk abu gudane.domin shehu Tijjani jikane ga Manzon Allah saboda haka sune Ahlussunnah na hakika a iakace.

Haka shima shehu Ibrahim inyass a son iyalan gidan manzon Allah to, shima ba' barshi a abaya ba.domina a littafinsa wanda ya wake manzon Allah { Diwani} bai gushe ba sai da ya kawo wadannan khalifofin nan 12 da manzo ya ce ''abi su'' ya yi musu kirari kuma kuma yayi tawassuli da su, daya bayan daya. wato shima umurnin manzo bata wuceshi ba kenan {saboda yasan darajarta} don haka shima shehu Ibrahim Inyass {RA} Babban Ahlussunna ne.

A cigaban wannan hadisin dai manzo na cewa ''kashedinku da kikirarrun al'amura,domin dukkanin kirkira bata ne.kuma dukkan bata yana cikin wuta'' {kada fa mu manta, manzo kirkira ya ce, ba jaddadawa ba} Abu dauda da turmizi ne suka ruwaito wannan hadisin. kuma ance ingantaccene.
to, har ila yau dai inda ake yawan samun matsalar shine wajen fahimtar ainihin ma'anar kalmar ta Bidi'a to, kunga a shimfidar hudubar malamin shima ya ce ''duk wata bidi'a batace kuma duk bata tana cikin wuta''. baicin ba haka manzo ke nufi ba.
[kune kawai kuka fahimci kalmar a haka} lalle anan in har malam ya fahimci hikimar magana irin ta manzon Allah cikin wannan hadisin to bai kamata shima malam ce '' Duk wata bid'a bata bace, kuma duk bid'a tana wuta ba''

Farko ai akwai ayar al'kur'ani da hadisai da suke magana a kan {THANNA} wato kirkira na wani abu sabo a addini 'Introducing' kamar a suratul An'am aya ta 160 Allah {SWA} ya cewa ''wanda yazo da kyakkyawar aiki guda yana da lada goma din misalinsa. kuma wanda ya zo da mugun aiki guda baza'a saka masa ba face da misalinsa.kuma su ba'a zaluntarsu''

Manzon Allah yana cewa ''Duk wanda ya faradda wani abu a misulunci na wata sunna kyakkyawa, to, yana da ladar ita wannan sunnar,kuma yana da ladar wanda yayi aiki da wannan sunnar bayansa, batare da an tauye daga nasa kason ba''muslim ne ya ruwaito wannan hadisin, a shfi na 93 cikin littafin Bugyatul musulumina.

To kaga idan muka yi la'akari da wannan Ayar Al'kur'anin da kuam wancan hadisin ,to lalle duk wani aiki wanda ba manzo ya yi shi ba, kuma bai ce ayi ba, kuma bai ga ana yi yayi shiru ba. har dai idan dukkan bid'ane bata kuma yana cikin wuta to, bari mu dauki salatil-fatihi mu yi misali da ita.a kwai wasu bangaren musulmi da su suke jincewa ''su ba su yarda da salatil-fahtihi ba da kuma mai yinta. har ni da kaina na taba jin wani dan izala yana cewa ''shi zai iya bin kowa salla banda mai karanta salatil-fahtihi'' akwai kuma masu dauakar ma'abota salati-fatihi a matsayin mushirikai, akawi kuma masu kafirta su bisa tasu hujjojin.har a kwai masu cewa '' sun san Iyayensu mahaifa suna wuta yanzu haka'' wai suna tayasu al'hinin hakan, saboda sun mutu suna darikkkka suna karanta salatul fahti'' wannan shi zai nuna mana cewa mafiya yawan wadannan mutanen basu yarda da salatil-fatihi ba.

To, amma indai a Nigeriya ne ga wanda ya kai shekara arba'in 40 da wani dan doriya to, kusan ya girmi izala a kasarnan. { ya wancin jagororin izala} kuma mafi yawanku sai da aka karanta salatil-fatihi a wajen daura auren iyayaensu { tunda daia alokacin babu izala} kuma yanzu kunce karanta salatin-fatihi shirka ne ko ma kafirci. to, munji amma ga tambaya;- An taba daura aure ga musulmi da wani abu daga shirka ko kafirci? amsa ita ce, A'a. to idan hane { yanda kuka ce} Auren mahaifiyarku da mahaifinku baiyyi ba kenan {tunda dai ana karanto salatil fatihi a daurin auren}
Ga wadansu tambayoyi uku. 1, to mene sunanku kenan {tunda a daurin aure bayyi ba saboda salatil fat?} 2, yaya kuke cin gadon iyayenku idan sun mutu suna darika bayan kuma kunce duk mai karanta salatil-fatihi mushirikine ko ma kafiri? 3, meyasa kuke daukansu a matsayin iyaye, bayan kyma auren ma bayyiba tuna an karanto salatil fatihi a daurin auren { kamar yadda kukace} tunda dai kunce dukkanin bidi'a batace. to, ga abin lura munsan Manzo bayyi salatil-fatihi ba. to ga wata tambayar;- yace kar ayi?!!!
to amma ai aakikn da manzo bayyi ba ba hujja bace a musulunci, hujja shine abibnda akeyi manzo ya gani kuma ya hana a yi, to, shine hujja. tabbas abinda manzo baice ayi ba kuma baiga ana yi yayi shiru ba to shine bidi'a, to amma a bidi'an ma akwai mai kyau akwai mummuna kamar yadda yake a bidi'an ma { HERESY} a turance na amu'amullar yau da kullum, kuma akwai bidi'a na Addini. kuma lalle idan aka ce ''duk kirkirarren abu bidi'ane kuma kuma yina wuta to ai kaga babu amfanin waccan ayar ta suratul ma'ida-160 kenan. da kuma hadisin muslim da na kawo a baya kenan, kuma lalle hakan ba mai yuwuwa bane. ni a nawa 'yar fahimtar da manzo yayi cewa bayan shi sai Ali aka ki bin wannan wasiyyar aka juya baya gameda khalifofinan 12 kuma ya ce aso iyalan gidansa mafi yawan mutane suka ki! sai kalilan suka amsa wannan ummurni ta manzo {'yan shi'a}mafi yawan mutane suka ki. sukaje suka kama Abubuwanda ba su Allah da Annabi suka ce a bi ba. karara aka sabawa maganar manzon Allah aka kama sababbin Abubuwa kirkirarrua cikin Addini lalle a nawa Fahimtar shine Manzon Allah yake nufi da ''kirkirarrun al'amura'' wanda har akwai hadisi musamman inda manzon yake cewa '' wanda yaga wani abu da babu shi a cikin al'amarimu {Addini} to ba za'a karba masa ba.bahari da muslim ne suka ruwaito wannan hadisin. a wata ruwayar kuma ta muslim ya ce;-'' wanda yayi wani kin da baya cikin ummurninmu to, aikinsa yazama ba karbabbe ba''hadisi na biyar cikin littafin ar'ba'una hadis. saboda haka ni a tawa fahimtar duk wanda yabi ummurnin manzo sau da kafa to shine Ahlussunnah ko da kuwa wata irin fahimta yake da ita.matukan dai yayi kalmar shahada ko da kuwa wata iri fahimta yake da ita. kuma dukkan wanda ya sabawa manzo ya kau da kai daga ummurninsa,kuma yabijire wa maganasa ya bi kirkira, ya ki 6yarda da sakon gadir da manzon Allah ya yi ummurni wanda ya ji ya fada wa wanda bai ji ba. uba ya fad wa dansa haka har ranar tashin kiyama ba. kuma ya ki da yarda da batun khalifancin Imam Ali ne farko bayan wafatin manzon Allah da gangar bawai don bai sani ba. kuma ya ki bada wulayarsa ga wadannan halifofo da manzo ya kira sunayensu daya, bayan daya kuma duk da gangar kila ma har da ikirarin karyatawa, wanda wadannan khalifofi su manzo yz kirasu da shiyayyu masu shiryarwa. ya kuma ce ayi ruko da sunnarsa, dakuma nasu a bayansa. duk mutumya tattara ya watsar kuma da gangar.
Cikin hadisai birjik manzon Allah yayi ummrni da aso iyalan gidansa tsarkaka wato {Ali,Fatima, Hassan, da Husaini AS} wanda har Al'kur'ani ke cewa ''Manzo baya neman mu biya shi da komai, game da wannan sakon da yazo mana da shi, sai dai kawai abinda yake bukata shine a nuna soyayya ga makusantarsa. ''malamai da yawa sun fassara makusanta da cewa sune iyalan gidan annabta'' wato { Ali, Fatima, Hassan da Huaini AS} kuma yazo ahadisan manzo bisa nuna sayya ga iyalan gidansa tsarkaka.kuma mutum yaki nuna wa da gangar, ta saba wa maganar manzo ko bai saba ba?
to, wanda yake sabawa ummurnin manzon Allah shine Ahlussunnah?
amsa kawsai wsannan shine babban da bidi'a!! idan ma akwai abinda yafi bidi'a to wannan mutum shine!!! kuma bidi'a batace,amma banda mai kyau b ko da kuwa manzo bai cea yi ba. idan kuwa manzo na nufifin duk bidi'a ne bata to da a wannan zamanin namu ba za'a iya samun dan al'janna ba, da duk wanda ya mutu da sai wuta kawai.
Ga wasu bidi'o'in 12 wadanda manzo be yi ba, kuma yanzu ana yi a mu'amula kai bama a Addini ba ma tukuna {Duk da cewa dai rayuwar mutum ma addinine} 1,manzo ya taba sanya wando irin namu da muke sakawa yanzu? ko jallabiya ko babbar riga aska biyu? 2,manzo yz taba jin rediyo ko ya ce aji? 3, manzo yanada fanka a dakinsa? 4, manzo ya taba kallon TV ko tashan 'Sitelite'? 5, manzo yznz shan sanyin AC? 6,ko manzo yanada wayar hannu {G.S.M} 7, manzo yznzda shafin yanar gizo 'Internet'? 8, manzo yznz da wutan lantarki a gidansa? 9, manzo yz taba kallon fim a bidiyo ko a CD? 10, kan famfo nawane a gida manzon Allah? 11, manzo yayi karatun boko idan ya yi digirinsa nawa, kuma me ya karanta? 12 manzo ya taba cin tuwo, ko teba? Tambaya an taba ce makam wadannan haramunne? amsa shine A'a sai da kawai bidi'ane amma masu kyau. don idan ya zama wadannan abubuwan duk bidi'a ne kuma duk suna wuta, kasan duk wada ke wannan zamanin shiga al'jannsa zai yi wuya kenan ko? { saboda haka ba ko wsacce bidi'a ce bata ba}

To, ga wadansu bidi'o'in har 12 wsanda manzo bayyi ba kuma bai ce ayi ba, amma gashi yanzu nan yi a Addini.
1, cewa rabbana wa lakal-hamdu a salla annabi yayi?
2, sallar tarawihi a jam'i annabi yayi?
3, sallar tuhajjut a jam'i annabi yayi?
4, hawa jirgin sama zuwa makka annabi yayi?
5, zama idan ana hudubar sallar juma'a annbi ya taba yi?
6, gasar karatun Al'kur'ani annabi yayi ummurni karara cewa ayi?
7, Annabi yayi wa'azin kasa?
8, kungiyanci a addini da yi wa kungiya rijista a 'CAC' annabi ya yi?
9, kwamitin masallaci fa annabi ya yi?
10, hawa mota zuwa wa'azi annabi ya yi?
11, kasuwancin kaya a filin wa'azi fa annabi ya yi?
12, wa'azi a rediyo,ko a TV annabi ya taba yi?

Duk wadannan abubuwan babu wanda manzo yayi ko daya daga cikinsu amma gashi yanzu duk muna yi. tambaya;- shin duk mun zama 'yan wuta kenan tuda duk bidi'a batace kuma duk bata yana cikin wuta? a naka fahimtar? lalle idan akak fassara wannan hadisin a wannan fahimtar taka to zai zama ba'a yi wa manzo Adalci ba.kuma lalle idan aka tafi kan wannan fahim ta taku to, zai zama kun kauda wasu ingantattun hadisai. kamar inda manzo ke cewa ''Duk wanda ya fardda wani a bu a musulunci na wata sunnahkyakkawa, to yana da ladar ita wannan sunnar,kuma yana ladar wanda ya yi aiki da wannan sunnar bayansa. ba tare da an tauye daga nasa kason ba'' muslim ne ya ruwaito wannan hadisin shafi na 93 a littafin bugyatl-muslimina. kaga kuwa bazai yuwu maganan wani ko fassarar wani ya share hadisin Manzin Allah ba. nasan ma'anar bidi'a ahausa dai shine sabon abu wato ' Heresy' a turance. to amma ba lalle bane ko wani sabon abu kawai sai ya zama bata. na'am yana iya zama bidi'a a suna kuma bidi'a kalmace ta larabci ba wsai ta takaitu a haramci bane kadai balantana yazama haramun. idan bamu manta ba ai ko da musulunci ya zo, ai akwai abubuwan da ya hana, kuma akwai abubuwanda bai hana ba saboda kyansu. kuma ana yisu tun kafin zuwan musunlunci, saboda haka akwsai bidi'a mai kayu akyau akawi maras kyau.
amma kuwa kaga shi kirkirarren al'amari muninsa yayi yawa shi yasa manzon Allah ya ce ''kashedinku da fararrun al'amura'' 1,anan bautun khlifanci kaga ai kirkirane tunda ba'a ba wanda manzo mya ce shi zai gaje shi a bayansa ba.2,hakana kuma an watsar da wassyyar manzo game da wilaya ga halifofin nan 12 {shiryayyu masu shiryarwa} 3, manzon Allah ya fada ya nanata cikin hadisansa cewa ''mu yi nruko da iyalan gidansa tsarkaka Ahlul-bait amma al'umma bama rukon da su ba kwata-kwata an ma jahilcesu ne gaba daya. amma sune kamar haka {Ali, Fatima, Hassan, da Husaini AS} an kirkiri wasu ya zama su kawsai ake bi, ba hakikanin abinda manzon ya gudanar a rayuearsa mai al'barka ba.kaga an bi kirkira an bar magana ko ummurnin manzon Allah {SAW} ''SUNNAH'' na hakika.
to, manzo dai ya ce ''kashedinku da kirkirarun Al'amura don dukkaninkirkira bidi'ace. kuma dukknin bidi'a bata ce,kuma dikkanin bata tanan cikin wuta'' Abu-dauda da tirmizi ne suka ruwsaito wanna hadisin, kuma aka ce hadidin ingantcce ne.
dalilina na yi wannan rubutu yana nan a littafin ar'ba'una hadis, hadisi na 34 an karbu daga abi sa'idul kudriyyu {RA} ya ce ''na ji manzon Allah {SAW} yana cewa wanda ya ga abin ki, to lalle ya canza shi da hannunsa,idan kuma ba zai iya ba, to ya canza shi da harshensa,idan kuma ba zai iya ba, to ya ki abin a zuciyarsa.a..a wannan shine mafi raunin imani'' muslim ne ya ruwaito wannan hadisin. ni kuma naga a gaskiya bana son in zama mai raunin imani, akalla idan ban zama na farkoba to, in zama na tsakiya mana. wannan dai shine da fatan mun amfana, ma'assalam!

Nura Ibrahim Khalil Zariya.
G . S . M 0803 371 8219.
nuriddeen2003@yahoo.com
khalilnuri@yahoo.com

No comments:

Post a Comment