Friday, December 29, 2017

KWANAKI 40 DA RASUWARTA; Wace ce Marigayiya Hajara Idris [Gwamma]?SHIMFIDA;
Na zabi sajjala wadannan ‘yan kalmomi ne saboda muhimmancin tarihi a rayuwar dan-adam. A lokaci guda kuma mai yuwuwa wasu su amfana da wasu abubuwa da ke ciki. Sannan ‘ya’yan marigayiyar da jikokinta masu zuwa za su ji dadin samun wannan tarihi a kammale. Musamman dayike muna lokaci ne na ‘internet’, matukar aka sanya shi a ‘net’ komin dadewa ana iya bincikawa kuma a sameshi. Ta fuskar taskace tarihi kuma, Sayyid Zakzaky [H] yana cewa; ‘’Da kiyaye tarihi ne al’ummomi ke sanin tarihin kawukansu.’’ Madalla da jagora abin koyi. Allah [T] ka kwato mana su kuma ka kara masu lafiya da kariya ta musamman. Masu sha’awar sake karanta wannan rubutu sai su shiga; http;//nuriddeen.blogspot.com

WACE CE MARIGAYIYA HAJARA IDRIS (GWAMMA)?
An haifi marigayiya Hajara Idris wacce aka fi sani da (Gwamma) a ranar alhamis 18/4/1985 a anguwar gwari da ke Suleja ta jihar Niger. bayan ta dan tasa sai saka ta a makarantar muhammadiyya. Bayan wani lokaci aka kai ta makarantar boko mai suna Ibrahim Dodo Priamary School. a dai garin na Suleja. ana cikin haka ne aka kai ta Kaduna wajen wata 'yar uwansu. bayan ta zauna a can na wani dan lokaci sai aka dawo da ita Suleja (garin ta na haihuwa). Ta kamala makarantar ‘primary’ a shekarar 2001 kuma a wannan lokaci ne aka yi mata aure. daga nan sai ta fara karatun 'Secondry' a Girlsday Secondry School, Suleja kuma ta kammala a shekarar 2007. bayan ta haifi 'ya'ya uku duk mata, wadanda suka hada da: Maryam, Surayyah da kuma Nusaiba, sai auren nata ya mutu. a wannan lokaci ne ta sake komawa hannun mai rukonta, dan uwan ta kuma yayan ta, wato Malam. Husaini Musa Barde. a hannunsa ne ta  fahimci harkar musulunci a Nigeria karkashin jagorancin Shaikh Ibraheem Zakzaky (H). a wannan lokaci ne ni Nura Ibrahim Khalil, Zaria na ganta na aure ta. ta haifa mani 'ya'ya hudu, mace daya, maza uku. Na faro ita ce Amina (Sister) ta rasu, Aliyu (Haidar) yana raye. sai tagwaye Hasan (Mujtaba) ya rasu, amma Husaininsa (Imam ko Ruhullah) yana raye. Hajara Idris na cikin matan da sojojin Nigeria suka kama suka kai su bariki tsawon kwanaki. a yunkurinsu na kai dauki gidan jagora a Gyellesu, Zaria, lokacin da sojojin suka kaddamar da harin kisan kiyashi kan 'yan uwa musulmi almajiran Shaikh Zakzaky (H) ranar 12 - 14 'December 2015 a Zaria. Hajara Idris harisa ce tsayayyiya kuma wakilya ce a inuwar mata almajiran Shaikh Zakzaky (H) wato fatimiyya forum na da'irar Suleja. sannan wakiliya ce a hadaddiyar inuwar mata na harkar musulunci a Nigeria reshen Suleja. ta rasu ne sakamakon jinya a dalilin haihuwan wadannan tagwaye. ta rasu cikin daren lahadi 1/3/1439H (19/11/2017).


SHAIDARMU AKAN MARIGAYIYA HAJARA IDRIS:
A littafin kanzul-ummal, juzu'i na 6, shafi na 217 hadisi na 3,819 Manzon Allah (S.A.W) yana cewa: "Wanda ke fatan ya rayu kuma ya koma ga Allah kamar ni, ya mika wilayarsa ga Ali Dan Abi-Dalib (AS))’’. Mun shaida Hajara Idris ta koma ga Allah tana da cikakken wilaya ga Amirul-muminina Ali Dan Abi-Dalibi (AS). ana kuma yin kyawawan mafarkai da ita. Marigayiya Hajara Idris tana da hakuri, kunya, yakini akan batun lahira, tausayi, tsafta da kuma himma ga duk abinda ta sanya a gaba. (takan so ba'a idan tana cikin nishadi). Kafin ita, ban taba cin wani abinci ko shan wata miya mai dadi kamar nata ba. kafin ta rasu ita ta fadi wadanda za su yi mata wanka, nau'in likkafanin da za a sa mata, makabartar da za a bisne ta da kuma wacce za ta rike 'ya'yanta wato Aliyu (Haidar) da kuma Husaini (Imam ko Ruhullah). ta kuma nemi yafiyata a duk wani laifin da ta yi mani kuma na yafe mata.

Muna rokon duk wanda ya karanta wannan rubautun ya yi wa wannan baiwar Allah salati goma ga Annabi [S.A.W] da nufin Allah [T] ya kai ladan ga ruhinta. masu sha'awar kasancewa a dandalin tunawa da marigayiya Hajara Idris Memorial Forum su ziyarci wannan shafi da aka kirkira tun ranar da ta rasu domin tunwa da ita: www.facebook.com/hajaramamarhaidar

JADDADA GODIYA TA DA BAN-GAJIYA
Ina jaddada godiya ga Allah (T) sarkin da ya yi rayuwa da mutuwa. kuma ina salati adadi mai yawa ga Manzon Allah (SAWA), Manzon da Allah ya aiko domin kyautata rayuwa da kuma inganta makoma. Ina kara jaddada godiya ta maras adadi ga 'yan uwa da abokan arziki na kusa da kuma nesa bisa samun damar halartar jana'izar mata ta Hajara Idris wacce aka fi sani da Gwamma, wacce ta rasu sakamakon jinya a dalilin haihuwa a daren lahadi, 1 ga watan rabi'ul-Awwal 1439H dai-dai da 19/11/2017. aka kuma yi mata jana'iza ranar litini da safe. Sannan ina jaddada godiya ga dukkan wadanda suka taimaka ta kowace siga, tun lokacin da ta fara jinya har lokacin da Allah ya yi mata cikawa. ba kuma zan manta da 'yan uwa mata ba, tun daga wadanda suka yi mata wanka da dukkan wadanda suka zo daga ko'ina. hazalika, ba zan manta da dukkan wadanda suka zo mana gaisuwa a nan Suleja da kuma wajen mahaifi na a gidanmu da ke cikin Zaria ba. ina kuma jaddada godiya ta ga abokai na na 'social-media' wadanda suka yi mani gaisuwar wannan rashi ta yanar gizzo. Harwalayau! ina kara godewa wadanda suka samu damar zuwa wajen addu'ar uku da aka yi, a nan Suleja da kuma can Zaria. A karshe ina kara jaddada godiya ta ga editan almizan Malam. Ibrahim Musa, ma’aikatan Al-wilaya TV Hausa, Mrs. Candy Stallworth, jami’ar yada bishara na addinin kirista da ke New York na Amurika, yaya na  Ahmad Ibrahim Khalil, Zaria da kuma kani na Shafi’u Ibrahim Khalil, Zaria da suka dauki nauyin karatun al-kur’ani da aka yi ga marigayiya Hajara Idris na cika kwanaki 40 da rasuwarta da wadanda uka karanta alkur’anin tare wadanda suka yi addu’ar 40 a gidanmu da ke Zaria, ‘yan uwan da aka hadu aka yi 40 a nan Suleja musamman madrisatu fudiyya, Suleja, ‘Yan uwa na majalisin ‘yan uwa na Halkar Imam Hasan Al-mujtaba [AS], anguwa Malam. Shehu, Suleja da sauran wadanda yanayi ba zai bari in ambaci sunayensu ba.
Nagode!!! Allah ya saka maku da jannatul-firdausi.

---Nura Ibrahim Khalil, Zaria (Baban Haidar/Mijin marigayiya)
29/12/2017 Hanyar tuntuba: 08033718219.


Tuesday, October 3, 2017

Karanta Hirarmu Da Dr. Zakariyya Mika'il

Wannan wata hira ce da muka yi  Dr. game da magungunansa na ma'u-shifa, center da ya bude da kuma yadda ayyukan nasa za su kasance, muna fata za ku kasance tare da mu. Nura Ibrahim Khalil, Zaria ne ya tattauna da shi. ga hirar tasu yadda take, a sha karatu lafiya.

Ko za mu niya jin sunan malamin?
Suna na Dr. Zakariyya Mika’il.
Ko za ka yi yi mana dan takaitaccen bayani game da kanka?
Na’am! Nine manajan Daraktan Cibiyar da ke fitar da magungunan gargajiya da sunan ma’u-shifa da ke garin Suleja.
Mene ne sunsn wsnnsn ciniya taka?
Suna wannan cibiya tawa shi n; ‘Halal Herbal Medicine and Reserch Center ‘ kuma muna fitar da magungunanmu ne da sunan Ma’u-Shifa.
Ko za mu iya jin dalilanka na bude wannan cibiya?
Na farko dai duk da cewa magungunan namu sayarwa muke yi, amma dai mun san cewa; ‘’Duk wanda ya taimaki wani har ya samu lafiya, yana da lada mai yawa’’ na biyu, kuma mun lura ne dayawan mutane suna tafiya da cututtuka a jikkunansu amma basu sani ba. Sannan magungunan da suke amfani da sub a kowanne bane yak e basu abinda suke so. Na uku kuwa shi ne muna sa ran idan wannan cibiya tamu ta bunkasa, muna iya zama dalili na samar wa matasanmu da aikin yi a wannan cibiya tamu.
Wane irin tabbaci za ka ba jama’a game da ingancin yadda kake hada wadannan magunguna naka da kuma hanyoyin da kake bi wajaen hada su?
Na farko dai kafin fara hada wadannan magunguna da kuma bude wannan cibiya tawa, na shafe akalla shera shida ina bincike akansassan jikin dan-Adam da ciwuwwukan da ke damunta da kuma irin magungunan da ake amfani das u wajen warkar dad a wadannan cututtuka. Sannan masu cututuka daba-daban sun yi amfani da magungunanmu suna ta godiya. Akwai magungunan da muka hada, yanzu haka yana kasuwa, kamar maganin asma, da maganin ulsa da kuma maganin ‘typhoid’. Sannan akwai magungunan da sai mai ciwon ya zo mun yi Magana sai mu yi masa hadi na musamman, musamman a irin cututtukan da suka hada da ‘toilet infection’ ko matsalar gocewar kwakwalwa da dai sauran matsalolin da suka shafi lafiyar dan-Adam. Saboda haka wannan cibiya tamu bata fito ba said a shirya, lallai magungunanmu suna da inganci saboda hadi ne na wadanda suka san ciwo kuma suka san san magani.
Ko akwai wajen da za a rika samun wannan magani naku,ya ake amfani das hi, kuma nawa ne farashinsa?
idan aka lura za a rika ganin magungananmu wajen masu tallanmu suna zagayawa da su da kuma a islamin chemists, kusan kala uku: na farko shine maganin typhoid wanda ya ke wa dan-adam maganin ciwuwwuka kusan shida. na farko shi ne zazzabin typoid din kansa. na biyu ciwon shawara, Na Uku Zazzabin Asma, Na Hudu Zazzabin Cizon Sauro, Na Biyar Rashin Iya Cin Abinci, Na Shida Rashin Kuzari.

yadda ake amfani da maganin maganin: babba ya sha gora biyu a yini, yara kuma su sha gora daya a yini. farashin wannan maganin mai suna ma'u-shifa cure for typhoid naira dari #100 ne kacal kuma insha'allahu idan aka yi amfani da maganinmu za a yi wa allah godiya. .....
sannan muna da ma'u- shifa cure for ulcer: shi kuma wannan maganin ulsa ne wanda aka yi masa hadi na musamman. sannan baya ga ciwon ulsa yana kuma maganin basir, shawara da kuma ciwon ciki.
yadda ake amfani da maganin: babba ya sha gora biyu a yini yara kuma su sha gora daya a yini. shima farashinsa naira dari ne #100 kacal. mutane da yawa sun gwada wannan magani sun yi wa allah godiya. ....
muna da ma'u-shifa cure for asma: harwalayau! wannan cibiya ta tanaji magani na musamman ga masu ciwon asma wanda maganin ciwon asma ne kai-tsaye amma a lokaci goda yana maganin ciwon hakarkari, matsalar numfashi, tari da kuma sanyi.
yadda ake amfani da maganin shine: babba ya sha gora biyu a yini yara kuma su sha gora daya a yini. duk da kyawun wannan magani farashinsa dai shima naira dari ne #100 kacal!
ko za mu ji alamomin kamuwa da wadannan cututtuka?
duk wanda zazzabin typhoid ta kama shi zai rika; kin son cin abinci, yawan ciwon kai, ciwon gabobin jiki, zazzabi mai kaiwa ma'aunin zafi 104 da kuma gudawa. ......
shi kuma zazzabin asma na haddasa, yawan zuban majina daga hanci, kaikayin ido, kaikayin baki, kaikayin jiki, yawan atishawa da kuma, yawan gajiya. .....
wanda ya kamu da zazzabin cizon sauro kuma yana kasancewa ne kamar haka: yawan makyarkyata, [ jin dari] da ciwon kai, sai tashin zuciya, amai da kum ciwon ciki. ....
alamomin da zai sa ka gane cewa ka kamu da ciwon ulcer sune. kuna mai radadi a ciki, idan aka jima ba a ci abinci ba ko kuma cikin dare, kunar zuciya, yawan hutu [tusa] sai tashin zuciya da kuma amai .......
shima wanda ya kamu da ciwo asma zai rika jin wasu alamomi kamar haka: yawan tari cikin dare, katsewar numfashi, zafin kirji, radadi a cikin kirji, da kuma yin wani irin numfashi mai kara kamar ana hura usur. .....
to! wadanne cutututuka ne ake samun ku don hada wa mutane magani na musamman kuma mene ne alamomin cututtukan?
toilet infection ne na farko; duk macen da wannan cuta ta kama ta, za ta rika ganin, farir ruwa na fitowa a gabanta, kuraje, jin zafi a yayi fitsari ko saduwa ......
sai matsalar kwakwalwa. muna da hadi na musamman ga masu masalar kwakwalwa wanda ke faruwa sakamako shaye-shaye wanda yanzu haka mun yi nisa a tattaunawa da gidajen da ke horar da kangararru don suna bukatar wannan magani na kwakwalwa.
ko kuna ganin mutane kan cututtukan da ke damunsu kamar yadda wasu cibiyoyin irin naku suke yi? eh! mu ma muna da wannan tsarin, mai kowane irin ciwo na iya samunmu domin hada masa magani na musamman akan farashi mai sauki. lambarmu ita ce: 08035786823 ...
ka ce kuna bada magani ga masu matsalar gocewar kwakwalwa, ko za ka yi mana takaitaccen bayani akan haka? kamar yadda na fai a baya, dayake akan samu masu samun matsalar kwakalwa akan dalilai daban-daban, kamar shan miyagun kwayoyi ko dalilin wani ciwo ko wani dalili na daban. to! idan muka ga mara lafiya ko aka yi mana bayanin yadda yake, insha’allahu idan muka hada masa magani ya yi amfani das hi kamar yadda muka tsara zai warke ya dawo dai-dai. bisa wannan dalilin ne ya sa masu cibiyoyin tarbiyantar da kangararru suke ta son hada karfi da mu domun mu riks samar musu da irin wannan magungunan kwakwalwa domin su rika samun sauki da kuma rage lokacin da ayyukan nasu ke daukansu.
wane kira kake das hi ga jama’a musamman masu son sayan magani mai inganci?
to! lallai mutum ya yi kokari ya jarraba maganinmu domin magani ne mai inganci kuma haryanzu bamu wanda ya sayi wannan magani namu ya koka ba saboda haka hausawa na cewa; ‘’sayen na gari, maid a kudi gida. kuma sunan magungunan namu gabaya shi ne ma’u-shifa.
ko kana da wani sako musamman ga masu ‘islamic chemist?’
sako nag are su shi ne duk mai bukatar sarin wadannan magunguna namu kofa a bude take, za mu bashi kan sari yadda zai amfana kuma muna tabbatar masa cewa mun inganta magungunanmu ta yadda shi mai sayarwa ba zai ji kunya ba. kuma sunan magungunan namu gabaya shi ne ma’u-shifa.
to! idan aka tashi nemanku a aina za a sameku?
muna nan a dapchi plaza, daura da mila-link, old u.b.a road, suleja, jihar niger.
mungo.
nima nagode.

Friday, September 15, 2017

GAME DA MASU NEMAN SANI AKAN MAGUNGUNAN MA'U-SHIFA TA DR. ZAKARIYYA MIKA'ILMA’U- SHIFA HALAL HERBAL MEDICINE AND RESEARC CENTER

Assalamu Alaikuma! Shahararren Cibiyar Nan Nan Mai Suna Halal Habal Medicine And Research Mai Fitar Da Magunguna Da Sunan 'Ma'u-Shifa' Ta Dr. Zakariyya Mika'il Bata Fito Ba Sai Da Ta Shirya Don Kawo Maku Ingantattun Magungunan Cututtukan Da Ke Damun Ku. ......

Dr. Zakariyya Shahararren Mai Bincike Ne Akan Harkar Kiyon Lafiyar Dan-Adam Kuma Kwararre Ne Wajen Hada Magun-gunan Cuttukan Da Ke Damun Al'umma A Wannan Nahiya Tamu. .....

GA KADAN DAGA CUTUTTUKAN DA KE YAWAN ADDABAN AL'UMA DA KUMA ALAMOMINSU:
TYPHOID: Duk Wanda Zazzabin Typhoid Ta Kama Shi Zai Rika; * Kin Son Cin Abinci * Yawan Ciwon Kai * Ciwon Gabobin Jiki * Zazzabi Mai Kaiwa Ma'aunin Zafi 104 Da Kuma Gudawa. ......

ALAMOMIN ZAZZABIN ASMA: Zazzabin Asma Na Haddasa * Yawan Zuban Majina Daga Hanci * Kaikayin Ido * Kaikayin Baki * Kaikayin Jiki * Yawan Atishawa Da Kuma * Yawan Gajiya. .....

SAI ZAZZABIN CIZON SAURO: Alamomin Wanda Ya Kamu Da Zazzabin Cizon Sauro Yana Kasancewa ne Kamar Haka: * Yawan Makyarkyata * Jin Dari * Ciwon Kai
 * Tashin Zuciya * Amai Da Kuma * Ciwon Ciki. ....

CIWON ULCER; Ga Alamomin Da Zai Sa Ka Gane Cewa Ka Kamu Da Ciwon Ulcer. * Kuna Mai Radadi A Ciki, Idan Aka Jima Ba A Ci Abinci Ba Ko Kuma Cikin Dare * Kunar Zuciya * Yawan Hutu [tusa] * Tashin Zuciya * Amai .......

ASMA: Shima Wanda Ya Kamu da Ciwo Asma Zai Rika Jin Wasu Alamomi Kamar Haka: * Yawan Tari Cikin Dare * Katsewar Numfashi * Zafin Kirji * Radadi A Cikin Kirji * Yin Wani Irin Numfashi Mai Kara Kamar Ana Hura Usur. .....

TOILET INFECTION: Duk Macen Da Wannan Cuta Ta Kama Ta, Za Ta Rika Ganin * Farir Ruwa Na Fitowa A Gabanta * Kuraje * Jin Zafi A Yayi Fitsari Ko Saduwa ......

 MATSALAR KWAKWALWA: Muna da hadi na musamman ga masu masalar kwakwalwa wanda ke faruwa sakamako Shaye-shaye.

 IDAN AKA LURA ZA A RIKA GANIN  MAGUNGANANMU  WAJEN MASU  TALLANMU SUNA ZAGAYAWA DA SHU,  KUSAN KALA UKU: Na Farko Shine Maganin Typhoid Wanda Ya Ke Wa Dan-Adam Maganin Ciwuwwuka Kusan Shida. Na Farko Shi ne Zazzabin Typoid Din Kansa. Na Biyu Ciwon Shawara, Na Uku Zazzabin Asma, Na Hudu Zazzabin Cizon Sauro, Na Biyar Rashin Iya Cin Abinci, Na Shida Rashin Kuzari.

YADDA AKE AMFANI DA MAGANIN MAGANIN: Babba Ya Sha Gora Biyu A Yini, Yara Kuma Su Sha Gora Daya A Yini. Farashin Wannan Maganin Mai Suna Ma'u-shifa Cure For Typhoid Naira  Dari #100 ne Kacal Kuma Insha'Allahu Idan Aka Yi Amfani Da Maganinmu Za A Yi Wa Allah Godiya. .....

SANNAN MUNA DA MA'U- SHIFA CURE FOR ULCER: Shi Kuma Wannan Maganin Ulsa Ne Wanda Aka Yi Masa Hadi Na Musamman. Sannan Baya Ga Ciwon Ulsa Yana Kuma Maganin Basir, Shawara Da Kuma Ciwon Ciki. YADDA AKE AMFANI DA MAGANIN: Babba Ya Sha Gora Biyu A Yini Ya Kuma Su Sha Gora Daya A Yini. Shima Farashinsa Naira Dari Ne #100 Kacal. Mutane Da Yawa Sun Gwada Wannan Magani Sun Yi Wa Allah Godiya. ....

MA'U-SHIFA CURE FOR ASMA: Harwalayau! Wannan Cibiya Ta Tanaji Magani Na Musamman Ga Masu Ciwon Asma Wanda Maganin Ciwon Asma Ne Kai-Tsaye Amma A Lokaci Goda Yana Maganin Ciwon Hakarkari, Matsalar Numfashi, Tari Da Kuma Sanyi.

YADDA AKE AMFANI DA MAGANIN SHINE: Babba Ya Sha Gora Biyu A Yini Yara Kuma Su Sha Gora Daya A Yini. Duk Da Kyawun Wannan Magani Farashinsa Dai Shima Naira Dari Ne #100 Kacal! Sai An Gwada Akan San Na Kwarai. ...

 MA'U SHIFA CURE FOR TOILET INFECTION: Wato Maganinmu Da Ke Warkar Da Cututtukan Da Ake Dauka A Ban-daki Na Gama-gari. Shi Wannan Bangare Akan Samemu Ne A Yi Mana Bayani Sai Ya Zama Mun Hada Wa Mutum Maganin. Kuma Lallai Idan An Sha Ana Warkewa. Muna Hada Wannan Magani Ne A Farashi Mai Sauki.

MA'U-SHIFA CURE FOR BRAIN PROBLEMS: Wato Magungunan Mu Da Ke Magance Matsalolin Kwakwalwa Musamman Wanda Ya Faru Sanadiyar Shaye-shaye. Muna Da Hadehade Na Musamman Da Muke Ba Masu Cibiyoyin Kula Da Kangararru Suke Aiki Da Su Kuma Ana Samun Dacewa.

(5)ADDRESS: Muna Nan A Dapchi Plaza, Daura Da Mila-Link, Old U.B.A Road, Suleja, Jihar Niger. ... Muna Da Ranakun Da Muke Ganawa Da Mutane, Mai Son Ganinmu Sai Ya Tuntubemu A Lambarmu Kamar Haka: 08035786823 Sai Kun Zo... ....

Mai Kowane Irin Ciwo Na Iya Samunmu Domin Hada Masa Magani Na Musamman Akan Farashi Mai Sauki. ... Kada A Manta Lambarmu Ita Ce: 08035786823 ...

TAKEN MU SHI: Sayen Na Gari Maida Kudi Gida.HIRA TA MUSAMMAN DA MALAM. ADAMU ITTIHADU, JALINGO DAGA BIRNIN NAJAF, TA KASAR IRAKI

Wannan wata tattaunawa ce da aka yi da Malam. Aadamu Ittihadu Jalingo, wanda Allah cikin ludufinsa ya albarkace shi da kai ziyara birnin Najaf da ke kasar Iraki domin halartar Amirul Muminina Ali Bin Abi Dalibi [as] da halartar bukin gadir da kuma gudanar da wasu al’amura. Nura Ibrahim Khalil, Zaria ne ya tattauna das hi, kada mu ja ku da nisa, ga yadda hirar tasu ta kasance.
Tara Da; Nura Ibrahim Khalil, Zaria
1. WANE SUNANKA? Adamu Ittihadu Jalingo.
2. DAGA INA KAKE? Ina Najaf dake kasar Iraqi.
3. ME YA KAI KA NAJAF? Naje Najaf ne ziyaran Amirul Muminina Imamu Ali [a.s] da halartan bukin idil Ghadir, Sannan in dama ya bada, zan ci gaba da Karatu insha Allah.
4. YA KA GA NAJAF? Alhamdulillah Gaskiya yadda naga Najaf ya burgeni sosai, yadda naga komai ana yi bisa tsari, ga Abubuwan ci gaba iri-iri, gidajen Mai zakaga Direba ne zai sauka ya matsawa motansa Mai na iya kudinsa, Sannan yaje ya biya, ba tare da ana kallon Kar ya qyara ba. Rayuwansu kuma duk Daya bazaka banbanta Mai kudi da talaka ba.
5. YAYA MUTANEN NAJAF SUKA KARBE KU? Alhamdulillah Gaskiya mutanen Najaf sun karbemu hannu bibbiyu, sun daukakamu, sun mutuntamu ,sun kyautata mana, Sunyi mana hidima sosai duk da ma dai muna nuna musu su Bari mungode Amma ina! Sai yi suke, musanman suna kallonmu bakaken mutane kuma daga wuri Mai Nisa mukazo na duniya, sun nuna mana ‘yan uwantaka na Addini Gaskiya.
6. KO MUTANEN NAJAF SUN SAN SAYYID ZAKZAKY (H)? Kwarai kuwa mutanen Najaf sun San Sayyid Ibrahim Zakzaky (H), Zan iyace maka ma ai Mutanen Najaf kaman basu San kowa ba a Nigeria sai Sayyid Zakzaky, Domin duk Wanda ya ji daga Nigeria muke sai yace Zakzaky Zakzaky, to Gaskiya dai Manya da yara maza da mata zance maka kusan ba Wanda bai san Sayyid Zakzaky ba, Domin ni har yanzu banga Wanda yace min bai San Sayyid Zakzaky ba, Su duk wani Dan Nigeria ma ai Zakzaky ne kawai.
7. ME MUTANEN NAJEF KE FADI GAME DA WAKI'AR ZARIA? Gaskiya mutanen Najaf musanman manyan malamai da muka gaggaisa dasu, Abu na farko dasuke tambaya shine wane Hali su Sayyid suke ciki, da irin tausayawa, suna nuna irin Jimaminsu da bakin ciki, atakaice dai Gaskiya mutanen Najaf sun tausaya wa ‘yan uwa na Nigeria ba Dan kadan ba dangane da abinda ya faru a Zaria, Don kowa addu'a yake mana cewa Allah ya saka mana, ya dauka mana fansa.
8. ME YA FI BURGE KA A NAJAF? Ba Abinda yafi burgeni a Najaf kamar yadda na ga aka kawata Haramin Amirul Muminin Imam Ali [a.s] da irin tsari da aka yi wa Haramin Don maziyarta, musanman Lokacin da na shiga cikin Haramin Amirul Muminina Imamu Ali [a.s] Naji dadi da ban taba jin Irinsa ba a Rayuwana, Nace yau nine a gaban Abul Hassanain? wasiyin Annabi, Mijin Sayyida Fatima [s.a] ai bansan Lokacin da na Farayiwa Imam Ali baitoci da kirari cikin harshen fulatanci ba.
9. MENE NE SAKONKA GA 'YAN UWA MASU BURIN ZUWA NAJAF? Sako dai Ba zai wuce shawari ba, tunda dai zuwa Najaf ya kasu Kashi-Kashi, kowa da dalilin zuwansa amma dai manyan dalilan da suke kawo mutane Iraqi sune Ziyara Ko Karatu, to koma dai mene ne mu dai ‘yan harka ne a duk inda muke a duniya, to shawarin da Zan ba masu zuwa shine in Allah yayi mutum ya zo, Najaf Ko karbala, ya tsaya akan Abu guda Biyu kowa yasanshi a Haka, Karatu da Ibad , mekake yi Karatu, ko Ibada, Wannan dai shine shawari na.
10. MENE SAKON KA GA GWAMNATIN NIGERIA? Sakona ga Gwamnatin Nigeria, shine su sani fa cigaba da tsare Sheikh Ibraheem Zakzaky da matansa da harbi a jikinsu rashin Imani ne da rashin sanin mutunci ‘Dan Adam, tunda Sheikh Zakzaky bai musu laifin komai ba, duniya Tana gani ta kuma ta shaida, kuka je da rana tsaka har gidansa kuka kashe masa ‘ya"ya 3 kuka kashe masa ‘yan uwa, kuka kashe masa Al-majirai , a qarshe kuka harbeshi da matansa, kuka hana akai su asibiti, kuma wai Kuna zargin sa da laifi!!! Wa'iyazu Billah! Wallahi gaggauta sakin Sheikh Zakzaky da Iyalansa da Almajiransa shine zaman lafiyanku azzaluman banza azzaluman wofi, masara Imani da tausayi, ko kuso Ko kuki ko ku saki malam Ko karku saki Sayyid Zakzaky Wannan da'awan tasa za ta yi nasara, sai dai bakin ciki ya kasheku matsiyata.
11. MENE NE SAKONKA KHASATAN GA 'YAN UWA MUSULMI ALMAJIRAN SAYYID ZAKZAKY (H)? Sakona ga ‘yan uwa khassatan shine mu dauki Wannan Jarabawa a matsayin babban nasara a tare damu, su azzalumai suna ganin kamar mu suka harba, ko suka raunata Ko suka kashe, to Wallahi ba haka bane, kansu ne suka harba, sarautar sune suka jikkata, mulkinsu ne suka kashe, Sabo Da Haka mu kara dakewa Kar mu ji komai, mu tsaya kyam kamar yadda Su Sayyid suka barmu, kuma baza mu daina matsawa azzaluman Gwamnatin Nigeria ba har sai ta sake mana Jagoranmu , Allah kuma ya bamu sabati.
12. WANI SAKO KAKE DA SHI GA AL'UMMAN NIGERIA BAKIDAYA? Sako na ga al'umman Nigeria da farko dai ina musu barka da sallah, da Idil Ghadir, Sannan mu zama masu baiwa masu Kiyayya damu dubban kofofi da zai sa su zama masoyanmu, sannan kar mu yi sanadi ko dalilin samar da wata kofa koda guda Daya ce da zata sa masoyanmu su zama makiyyanmu, mu zama masu kiyaye hakkokin junanmu, mutunci Dan Adam da sanin ya kamata.
13YA KAGA BUKIN GHADIR NAJAF? gaskiya bansan ma yadda zan fara kwatantawa ba, Domin duk yadda na tuna Zan fada sai Inga ban fadi komai ba, Amma dai Lallai na ga babban bukin Idi mafi girma a Duniya, Wanda zan ce ya tara mutane diga kowace kusurwa ta Duniya, Lallai Ranar Idil Ghadir, Haramin Amirul Muminina Imamu Ali [a.s ] ta cika ta batse da Jama'a, Kai kace duk duniyan ne aka taho Najaf.


Friday, March 10, 2017

Masu Murnar Dawowar Buhari Sun Yayyage Mana Fastoci A Suleja


Yau juma’a 10/03/2017 ne aka tashi da labarin cewa shugaba Muhammadu Buhari na Nigeria ya dawo daga jyar da ya tafi a kasashen waje kimanin wata daya da rabi da suka wuce.

Kamar yadda kusan kowa ya gani a garuruwansu shi ne masoya shugaba Muhammadu Buhari sun cika gari da kide-kide da wake-wake domin bayyanar da murnarsu akan dawowar tasa.

Muna a nan Suleja ta jihar Niger hakan take domin mun tashi ne da irin wadannan shagulgula yayin da wasu ke kide-kide, wasu na raye-raye wasu sun shafa bula, wasu bakin tukunya suka shafa a fukokinsu suna munrnar dawowar tasa. sai dai Mafiya yawan wadanda ke wannan murnan matasa da yara ne maza da mata wato wadanda basu yin cefane ballantana su san cewa kayan masarufa ya yi tashin gwauran zabi.

Abin dai bai tsaya a nan ba, sai al'amari ya koma kan  ‘yan uwa musulmi al’majiran Shaikh Zakzaky [H] inda wadannan zauna gari banza suke bin wuraren da ‘yan uwan ke zama kamar anguwar iya, anguwar magaji har ma da daya daga cikin makantun da ‘yan uwa ke da shi a garin na Suleja wato Madarisatu Amirul-mumineen [AS] wanda ke anguwan Kabula ko Mila-Link suna zagin ‘yan uwa cikin ife-ife da kade-kade suna cewa; ‘’Babu shi’a, Buhari ya kashe ‘yan shi’a, shi’a karya ne.’’  a lokaci guna suna yayyage hotuna da kuma fastocin da ‘yan uwa suka mammana a wadannan wurare nasu irin su fastocin free Zakzaky da kuma na munasabobi da ‘yan uwa ke mannawa lokaci-lokaci domin ci gaba da rayar da al’amarin adinin musulunci.

Wani babban hujja kuma abin ban sha’awa shi ne duk wadannan cin mutunci da tsokana da wadannan zaun-gari-banza suka yi ‘yan uwa almajiran Shaikh Zakzaky [H] na wajen mutanen gari ma na kallo amma almajiran Shaikh Zakzaky [H] basu tanka wa wadannan zauna-gari-banza da komai ba.

Babu shakka wadannan mataki da ‘yan uwa suka dauka ya dauki hankalin mutanen gari kuma hakan ya basu sha’awa kuma lallai wasu sun nuna alamun tausawa. Wannan kuma ya kara nuna wa al’umma cewa muna da tsari.

Duk da cewa ‘yan uwa na da masaniyar cewa; Shaikh Yakubu Yahaya Katsina ya sanar da ‘yan uwa cewa; ‘’Sun tsara wannan al’amari ne domin a sanya zauna-gari-banza su tsokani ‘yan uwa.’’ sannan Shaikh Yakubu Yahaya ya jawo hankalin ‘yan uwa da cewa; ‘’ Kada a biye musu’’.

Idan dai ba a manta ba a ranar asabar  zuwa litini 12-14 ga watan disambar bara ne rundunar sojin Nigeria ta kaddamar harin babu gaira babu dalili kan ‘yan uwa musulmi almajiran Shaikh Zakzaky [H] bisa zargin cewa an tare wa tawagar Tukur Yusuf Buratai Hanya [wanda wannan al’amarin shiryayyen abu ne kawai] wanda a sanadiyar haka aka kashe ‘yan shi’a fiye da dubu daya aka jikkata da dama sannan aka harbi Shaikh Zakzaky da mai dakinsa malama Zeenatuddeen aka kuma kashe ‘ya’yanta uku aka rusa masa gida kuma ake tsare da Shaikh Zakzaky din tare da matar tasa ba bisa ka’ida ba. sannan aka rushe gine-gine,  aka kona kadarori, al’amarin da masana shari’a ke kallonsa a matsayin take hakkin bil’adama domin kotu ta yanke hukuncin cewa a saki Shaikh Zakzaky da matarsa a biyasu diyya kuma IMN ta ci gaba da gudanar da harkokinta kamar kowani dan Nigeria domin tsarin mulki na 1999 sashi na 38 da kuma na 40 ya baiwa kowa dan kasa damar yin addinin da ya ga dama, amma har yanzu shuru kake ji.
Allah [T] ya saka mana.

Don neman sani akan ayyukan IMN ana iya shiga www.harkarmusulunci.org ko www.islamicmovement.org
Tuesday, March 7, 2017

Tsarabar Hotuna Daga Gidan Adana Kayan Tarihi A Niamey Ta Jumhuriyar Niger


AL-KUR’ANI;  ‘’SIRU FIL  ARDI, FANZIRU KAIFA KANA AKIBATALLAZINA MIN KABLIHEEM.’’
Allah [T]  cikin alkur’ani  mai girma yana cewa;  ‘’Ku yi tafiya a doron kasa, za ku ga yadda makomar wadanda suka gabacesu ya kasance.’’
‘ Manzon Allah Muhammad [SAW] yana  na cewa; ‘’ Da kun san alhairin da ke cikin tafiya da kun kwana wayi gari kuna matafiya. ‘’
 Dr. Abubakar Imam yana cewa;  ‘’tafiya mabudin ilimi.’’
Saikh Zakzaky [H] yana cewa; ‘’ Daga kiyaye tarihi ne aluma ke sanin tarihin kanta.’’

Na samu damar zuwa birnin Niamey da ke jamhuriyar Niger domin gudanar da wasu alamura na ‘yan wasu kwanuka. A ranar asabat 6 ga watan jimada-thani shekara ta 1438BH dai-dai da 04/03/2017 Allah [T] ya bani ikon kai ziyara babban gidan ajiye kayayyakin tarihi da namun daji wato ‘National Museum’ ko kuma ‘Musee National’ [ BOUBOU HAMA] da ke Niamey ta jamhuriyar Niger. Na ji dadi sosai domin ni mutum ne mai sha’awar ganin kaya da wuraren tarihi. A wannan gida tarihi nag a abubuwar da ban taba ganin su ido da ido bat un da Allah [T] ya halicce ni sai a wannan rana.

Tsarin shiga wannan gidan adana kayan tarihi dais hi ne; idan maziyarci ya shigo kofar  wannan wuri zai ga dansanda tare da kwandon kudi da rasidai a gabansa. Mai ziyara zai je wajen wannan dansanda y ace; ‘’ Na zo ziyara ne’’ kuma maziyarci na iya na iya amfani da harsen hausa, zabarmanci ko faransanci. Daga nan wannan dansanda zai shaida maka nala arba’in ake biya wato F200 na kudin Niger, kwatankwacin naira dari da tamanin 180 na kudin Nigeria a canjin ranar 1438BH dai-dai da 04/03/2017.
Bayan bayar da wannan kudi wannan dansanda zai ce maka bisimillah! Wato [ka ci gaba da abinda ya kawo ka].    
To! Gaskiya dai wannan gidan adana kayan tarihi waje ne mai girma kuma akwai gine-gine irinsu ofisoshi, masallatai, gidajen  abinci, dakin daukan sauti ‘studio’ keji-keji na dabbobi  iri-iri tare da sheke-sheken furanni iri daban-daban masu ban sha’awa.
Mutane ne mata da maza, yara da manya ko kuma mata da miji da ‘ya’yansu kan zo wannan wuri akodayaushe don samun nishadi, wasu ma kan zo tabarmi ko dardumomi na salla, abinci da ruwa domin wasu kan wuni zungur ne a wajen, a yayin da wasu kan shagalta ne da daukan hotuna musamman ma sabbin zuwa.
[1] ABU NA FARKO; Abinda mai ziyara zai fara gani shi ne kejin nau’ikan tsuntsaye a ciki, a kusa da wannan keji wani allo wato ‘sign bord’ dauke da hoton aku, tare da sunyen akun cikin yaruka kusan biyar. Kazalika cikin kejin day a fi girma akwai nau’ikan tsintsaye kusan goma ciki kuma hard a wani zakara mai kafafuwa uku. A wani karamin keji da ke gefe kuea tantabaru ne da kurciyoyi ne a ciki.
[2] ABU NA BIYU;  Abinda za ka ci karo da shi kuwa shi ne zaki, amma gaskiya an kyautata ingancin karafunan da aka yi masa keji ko da daki das hi tare da matarsa. Kana iya matsawa kusa ka kallesu su ma su kallekahar ka yi masu hotuna ko bidiyo, dayike karafunan da aka yi masu wannan kejin da su hawa biyu ne [akwai na farko akwai kuma na biyu] a na biyun ne masu kallo ke tsayawa. Shi kuwa zaki da mai dakin sa wato zakanya sun ci nama sun bar abinda ya yi sau, sai namijin zakin na ta zagaye dakin matars tasa ku tana kwance a gefe tana shatawa duk suna kallo maziyyyartarsu.

[3] ABU NA UKU;  Keji zan ce ko daki na macizai, shi dai wannan wuri an yi shi kamar gidsn kasa ne sai aka gina shi kamar daki kuma aka yi masa raga na karfe  mai kananan huji ta yadda babu yadda macizan za su iya fitowa ta wadannan huje-huje ta yadda idan ka leka  za ka iya hango abubuwan da ke ciki kuma da wahala macizan da ke cikin wannan dakin na kasa su iya cutar da mai kallo saboda zufin wannan wuri.
[4] ABU NA HUDU; Shi ne mugun dawa suma mace ce da namiji ne kuma an tsara masu wajensu kamar wata gada ko idan suna bukatar sanyi akwai akwai inda za su shiga ruwa su yi wasa da ruwa idan kuma a tudu suke bukatar tsayuwa akwai wajen da za su je su tsaya. An kuma yi wani gini ne a ciki dab akin ramin ta yadda sub a za so iya fitowa ba mai kallo kuma ba sai iya fadawa ba sai dai idan ya yi matukar wuce gonad a iri.
[5] ABU NA BIYAR;  Tsarin da aka yi wa jimina shi ne an zagaye wajen da take da waya irin wanda ake zagaye gidan gona kuma an yi shuke-shuke daban-daban domin ya bata inuwa an kuma aje mata abinci da ruwa kammar yadda ake yi wa dabba a wajen.  Kana iya kallonsu ta raga dayike bas u da wani hadari.
[6] ABU NA SHIDA; Wani tshon kare ne  shima yana cikin wani keji ne tare da abincinsa maziyarta kuma suna kallonshi ta raga.
[7] ABU NA BAKWAI; A kwai wasu dakuna da aa killace wasu nau’ukan birrai ne kusan nau’I biyar kowa kuma yana dakinsa daban. Suma ana iya kallonsu ne ta raga.
[8] ABU NA TAKWAS;  An yi wa wasu kadoji tsari ne kamar yadda aka yi wa macizan da na bada labarin su a baya. Sai dais u kadojin an samar masu da ruwa kuma ba’a rufe masu saman ramin dakin da komai ba.
[9] ABU NA TARA; Akwai abinda ake cewa beguwa, baka ce mai yarfin fari-fari  ita ma dai an tsara mata ne kamar yadda aka yi wa kadoji.
[10] ABU NA GOMA;  Wani daki ne da ked a manyan zakuna mace da namiji, suma an tsara masu wajen ne kamar aka yi wa zakunan da ke farkon shigowa.
[11] ABU NA GOMA SHA DAGA;  An killace wata kura a wani daki tana rayuwarta  kamar yadda aka killace zakuna cikin natsuwa da yyalwateccen abinci.
[12] ABU NA GOMA SHA BIYU; Ba a bar kunkuru a baya ba domin shima an yi masa wani dan gini hawa hudu an aje masa abincin da yake bukata.
[13] ABU NA GOMA SHA UKU;  Akwai irin su gada da sauran wasu kananan dabbobi na daji suma a killace kamar yadda aka yi wa sauran dabbobin.
[14] ABU NA GOMA SHA HUHU;  A tsakiyar wannan wuri akwai wani farfajiya mai tsawon gaske a wurin kuwa an ajiye kwarangwal din halittannan ne da ake cewa ‘dragn’ har iri biyu.
[15] ABU NA GOMA SHA BIYAR;  Akwai wata busashshiyar  itaciya da aka yi wa tanti kuma aka gyara inda take an ce itaciya ce mai tarihin gaske.
[16] ABU NA GOMA SHA SHIDA; Akwai dakin daukan sauti  wato ‘studio’ kuma wannan daki cika yake da kayan kide-kide na gargajiya  kuma kana iya ganin abubuwan da ke cikin dakin don kana iya kallon abubuwan da ke cikin dakin daga waje sabada ginin gillas aka yi wad akin.
[17] ABU NA GOMA SHA BAKWAI; A wata ‘yar kasuwa a cikin wannan wuri inda ake sayar da kayyayakin gargajiya da ake yin su a wajen, irin su takalma, jakkuna, zobuna, abun wuya na mata har ma da gumaka.
[18] ABU NA GOMA SHA TAKWAS; Awai wajen was an yara yara wadda aka yi masa tsari kamar na ‘yan makaranta kuma an ce wajen baya rabo da yara musamman asabar da lahadi.

Atakaice wannan shi shi ne dan abinda na samo wa masu karatunmu domin a dan kara samun masaniya dangane da abinda ya shafi wannan wuri, domin kowa na iya samun wata dama ta yin irin wannan tafiya zuwa Niamey, idan yana da sha’awa yana iya lekawa wannan gidan ajiye kayan tarihi domin ya sha kallo kuma ya kara samun darrusa.
Lallai na yaba wa jamhuriyar Niger wajen rawar ganin da take takawa don raya aladun gargajiya da kuma adana kayan tarihi. Kamar dai yadda na fadi a farko  Saikh Zakzaky [H] yana cewa; ‘’ Daga kiyaye tarihi ne aluma ke sanin tarihin kanta.’’ To lallai jamhuriyar Niger tana kokarin kiyaye tarihin al’umarta.
Ina fata kasarmu Nigeria ma za ta kara ba irin wadannan wuraren tarihi muhimmanci  ta yadda zai zama masu son kawo ziyara Nigeria  za su karu kuma za a samu Karin kudaden shiga sannan zai zama an kiyaye tarihin yadda ya kamata. Da fatan wadanda abin ya shafa za su lura.
Na barku lafiya, sai wani jikon.
Nura Ibrahim Khalil, Zaria
E;mail;-inshaallahulkareem@mail.com
http;//nuriddeen.blogspot.com
+2348033718219
Asabat 6/Jimada-thani 1438BH [04/03.2017]

Ana iya ci gaba da kallon sauran hotunan...